07 September 2026
Ƙananan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a matakin Unguwanni sun fara cinikayyar ƴan wasa
Wasanni
About
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan yadda ake cinikayyar ƴan wasa a matakin ƙananan ƙungiyoyin Unguwanni. A yanzu dai ƙananan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da ke buga wasanni a matakin Unguwanni a jihar Kaduna, tuni suka rungumi tsarin cinikayyar ƴan wasa domin ƙarawa ƙungiyoyinsu ƙarfi.
Wasu daga cikin masu horas da irin waɗannan ƙungiyoyi sun ce wannan tsarin cinikayya ya taimaka wajen kawo ƙarshen rigingimu da a ke samu kan ƴan wasa, sannan kuma ana gudanar da ita ne kan kuɗin da suka fara daga naira dubu 30 zuwa sama.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............