
30 October 2025
Ra'ayoyin masu saurare kan janye wasu daga cikin jerin mutanen da Tinubu ya yi wa afuwa
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
About
Wataƙila sakamakon matsin lamba daga al’umma, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake bitar afuwar da ya yi wa mutane sama da 170 da ke ɗaure a gidajen yari saboda laifukan aikata kisan kai, fataucin miyagun ƙwayoyi da dai sauransu.
Shin me za ku ce dangane da wannan sabon mataki na shugaba Tinubu da ke tabbatar da cewa mafi yawan waɗanda aka yi wa afuwar a farko wannan wata, a yanzu za su ci gaba da kasancewa a gidan yari?
Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai cikin shirin Ra'ayoyin ku masu sauraro na wannan rana.
Latsa alamar sauti domin sauraren shirin....