
Send us a text
Batun samar da ‘yansandan jihohi na ƙara ɗaukar hankalin ‘yan Najeriya, musamman a dai-dai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Sai dai, samar da ‘yansandan jihohi ba abu ne mai sauƙi Kamar yadda wasu ke tunani ba. Gwamnatocin jihohi na buƙatar abubuwa masu yawa kafin su iya ɗaukar wannan nauyi, banda batun samar da dokar samar da wadannan ‘yansanda, akwai batun samar da kayan aiki da horo da sauran abubuwa da ake bukata don gudanar da dawainiyar ‘yansandan.
Babban abun da jihohi ke bukata don samar da ‘yansanda shine kudaden gudanarwa don samar da wadannan abubuwa da na ambata.
Ko nawa kowacce jiha ke bukata don samar da ‘yansanda?
Ta wadannan hanyoyi za a bi don samar da wadannan kudade?
Wadannan da ma wasu amsoshin shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba akai.