Yadda manoma suka karkata akalar noman barkono bana a Najeriya
25 October 2025

Yadda manoma suka karkata akalar noman barkono bana a Najeriya

Muhallinka Rayuwarka

About

Shirin wannan makon zai tare ne a jihar Kano dake Tarayyar Najeriya, inda aka samu manoma da dama a wasu yankuna da suka duƙufa wajen noman barkono a wannan shekarar. Ba shakka sun yi aiki tuƙuru, kuma haƙarsu ta cimma ruwa duba da ɗimbim barkono da suka girba.

Wannan lamari dai ya tayar da hankalin waɗannan manoma, waɗanda sun sauya alƙibla ne saboda ganin yadda farashin amfanin gona dangin hatsi ya faɗi warwas a kasuwanni, kuma sun yi haka ne domin su more daga ribar da aka yi ta ci daga barkono, amma sai gashi lamarin ya yi musu ta leƙo ta koma.

A kusan ilahirin kasuwannin kayan gwari, gani za ka yi ga barkono, wanda kafin yanzu yake tamkar gwal, sai ga shi yanzu masu saye su na mai tayin da suka ga dama.

Masana sun yi ittifakin cewa, ba shakka rashin tsari da alƙibla wajen noma da kuma binciken halin da kasuwa  ke ciki sun taka rawa ainun a wcikin wannan matsala da aka samu.

Sai dai kuma, matsaloli na yanayi ma sun taka irin nasu rawar, domin akwai matsin lamba daga yadda tsarin ruwan sama ya sauya, da sauraan matsaloli da suka addabi ƙasar noma.

Matsalar yanayi da muhalli na mummunan tasiri akan ko wane irin nau’i na noma.

shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin, tare da Michael Kuduson.