Karfafa gwiwa ga jama'a su koma noma a jamhuriyar Nijar
25 April 2026

Karfafa gwiwa ga jama'a su koma noma a jamhuriyar Nijar

Muhallinka Rayuwarka

About

Shirin muhallinka rayuwarka na wannan mako zai maida hankali ne kan yanda ake karfafa gwiwa ga jama'a su koma noma don ita ce babbar hanyar dogaro da kai ta fuskar abinci.

Tun bayan halin matsin da jama'ar Jamhuriyar Nijar suka shiga biyo bayan juyin milkin soja da ta haddasa karamcin da tsadar abinci a cikin kasar aka rika zaburar da mutane su kama aikin noma musamman abincin da aka shigo da shi daga ketare Wanda ba a nomawa a cikin kasar irinsu shinkafa. Aka dai ce da rashin tayin ake barin arha, ganin yanda gwamnati ta kyautata wuraren da za a iya aikin noma a sassan kasar daban daban, mutane da yawa sun fada noman kuma hakika kwalliya ta fara biyan kudin sabulu.