
16 May 2026
Sauyin Yanayi ya jefa Manoma cikin ruɗani kan lokacin da ya dace su fara shuka
Muhallinka Rayuwarka
About
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon ya tattauna na a kan yadda samun saukar Ruwan Sama na farko a bana ya jefa manoma a jihohin Arewacin Najeriya cikin ruɗani dangane da lokacin da ya dace su fara shuka.
Wannan na zuwa ne a yayin da hukumar hasashen Yanayi ta Najeriya wato NIMET, da uma wasu masana ke gargaɗi game da yiwuwar ɗaukewar ruwan saman da wuri, lamarin da zai yi janyo tafka hasarar akasarin amfanin gonar da aka shugka da wuri.