Opens in a new window
Illolin karancin gonaki kusa da jama'a da yadda ya shafi burin bunkasa samar da abinci
25 July 2026

Illolin karancin gonaki kusa da jama'a da yadda ya shafi burin bunkasa samar da abinci

Muhallinka Rayuwarka

About

Sau da dama, masu burin shiga harkokin noma a Nigeria kan canza tunaninsu, sakamakon rashin samun gonakin da za su noma kusa da gari, lamarin da kan tilasta su jingine aniyarsu ta yin noma.

Gwamnatin Nigeria dai, ta sha kira ga ‘yan kasar da su koma gona, la’akari da yadda Allah ya albarkaci kasar da wadatattun filayen noma da kuma yanayi mai kyau da za a iya noma kowane irin nau’in kayan abinci.