Skip to content
Opens in a new window
Hukumar NIMET a Najeriya ta yi hasashen yiwuwar ambaliya a jihoh 13 na ƙasar
26 September 2026

Hukumar NIMET a Najeriya ta yi hasashen yiwuwar ambaliya a jihoh 13 na ƙasar

Muhallinka Rayuwarka

About

A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan duba sabon hasashen da Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya ta yi, game da yiyuwar samun matsalar ambaliyar ruwa a wasu jihohi 13 na kasar a wannan damunar.

A baya-bayan nan, hukumar hasashen yanayi ta Nigeria wato NIMET, ta sake fito da wani sabon hasashen yiyuwar ambaliyar ruwa a cikin watan Agustan wannan shekara, tsakanin ranar 11 zuwa 20 ga watan na Agusta, a wasu jihohi 13 na kasar.

Cikin sanarwar da ta bayar, hukumar ta NIMET, ta bayyana cewa hasashen nata, ya dogara ne kan adadin ruwan saman da ake fatan samu, da yanayin kasa tare da girman magudanan ruwa da kuma yawaitar madatsun ruwa.