Yunkurin juyin mulki a Nijar ya ci gaba da ɗaukar hankali a faɗin duniya.
Mu Zagaya Duniya
A wannan makon shirin Mu Zagaya Duniya ya yi waiwayen kan sukar kalaman shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya yi na cewa arewacin kasar ya fi amfana da manufofinsa, sai batun juyin yunkurin juyin mulkin Nijar da ya dauki hankali, sai rahoton MDD da ya gano katsalandan din kasashen waje ne ke rura wutar rikicin Sudan, sai luguden wutar da aka yi musaya tsakanin Amurka da Iran da ya janyo asarar rayuka.
A Najeriya, jam’iyyun adawa sun fara tsara yadda za su kayar da gwamnatin APC mai mulkin ƙasar ta wajen haɗakar da za ta fitar da ɗan takara ɗaya mai ƙarfi da zai iya gwabzawa da shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, inda
ƙungiyar G-100, wadda ta tsara wannan haɗaka ta kawo shawarar cewa duk wanda ya samu takarar, zai yi wa’adi guda na shekaru 4 ne kacal.
Haka zalika, ikirarin da shugaba Bola Tinubu ya yi cewa yankin arewacin ƙasar ce ta fi cin gajiyar manufofinsa na sauye-sauyen tattalin arziƙi ya janyo suka daga masu ruwa da tsaki, inda ƙungiyar al’ummar Arewacin ƙasar da wasu ƙungiyoyin yankin suka caccaki kalaman, su na mai cewa a maimakon cigaba, manufofin shugaban sun mayar da yankin arewa cibiyar talauci.
A gefe guda kuma, gwamnatin mulkin sojan Nijar zargi Ivory Coast, Benin, Faransa, Chadi da kuma ECOWAS da kitsa shirin kifar da gwamnati, biyo bayan wani bore da ya faru a ranakun 28 zuwa 29 ga watan Agusta, da kuma haifar da rarrabuwar kawuna, musamman a tsakanin rundunar soji.
Yayin da ake tsaka da damana har ma aka fara tunkarar alamomin kaka, har yanzu akwai wasu garuruwa 20 na yankin Damagaram da ba su samu saukar ruwan shuka ba a Ƙaramar Hukumar Gangara na gundumar Tanut.
Mafi yawanci damina Niger bata wuce wata 3 zuwa 4, domin dai tana ƙarewa a watan Satumba in ta yi tsawon watan Oktoba.
Domin jin cikakken shirin, latsa alamar sauti.