Yadda haɗakar ƙungiyoyi suka ƙaddamar da farmaki a sassan Mali
02 May 2026

Yadda haɗakar ƙungiyoyi suka ƙaddamar da farmaki a sassan Mali

Mu Zagaya Duniya

About

Shirin ya soma daga ƙasar Mali inda a ranar 25 ga watan Afrilun da mu kayi ban kwana haɗakar mayakan Abzinawa na FLA da na ƙungiya masu ikirarin jihadi ta  JNIM suka ƙaddamar da mugayen hare-hare a garuruwa huɗu na ƙasar da suka haɗa da Sevare, Kidal, Gao da kuma  Kati.

A garin Kati da ke zaman babban sansanin sojin ƙasar ƴan bindigar sun yi amfani da motoci shake da bama-bamai da manyan bindigogi inda suka kai hari kan gidan ministan tsaron kasar Sadio Camara tare da hallaka shi.

A kasar Chadi kuwa aƙalla mutum 42 ne suka mutu bayan ɓarkewar wani rikicin ƙabilanci da ya faro sanadiyyar taƙaddama tsakanin wasu mata biyu yayin da suke ɗiban ruwa a wata rijiyar bayan gari.

A Najeriya kuwa, ranar Alhamis ne kotun ƙolin ƙasar ta yanke hukunci kan rikicin cikin gida na jam'iyyun ADC da PDP.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin, tare da Oumarou Sani.