Shugaban Faransa ya bayyana halin da ake ciki a zirin Gaza a matsayin abin kunya ga duniya
Mu Zagaya Duniya
A yau shirin ya yi waiwaye kan bankado yadda wasu fitattun yan siyasa a Najeriya suka wawure makudan kudade tare da mallakar kadarori a Amurka, sai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da ta fara gwajin allurar Ervebo don daƙile cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo, da kuma fassarar kalaman shugaban Faransa Emmanuel Macron a babban taron MDD da ya bayyana halin da ake ciki a zirin Gaza na Palasdinu a matsayin babban abin kunya ga ƙasashen duniya.
Masu bincike da suka ɓanƙado yadda jami’an gwamnatin Najeriya na baya da na yanzu suka wawure makuɗan kuɗaɗen talakawa wajen sayen manyan gidaje na ƙasaita a Amurka, sun ce yaƙi da ta’addanci na daga cikin manyan hanyoyi da ake amfani da shi wajen satar dukiyar jama’a a Najeriya.
Haka zalika, kotun sasanta rikicin kasuwancin ta duniya dake birnin Paris na Faransa, ta yi watsi da buƙatar Kamfanin Sunrise da ya nemi Najeriya ta biya shi diyyar kuɗi dala miliyan 400.