
Daga cikin labarun da shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan makon ya kunsa akwai labarin matakin da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ɗauka na yin tankaɗe da rairaya a manyan hukumomin tsaron ƙasar, inda ya sallami manyan hafsoshin tsaron ƙasar, dai dai lokacin da rundunar sojin Najeriya ta ce ta samu nasarar kashe ‘yan ta’adda fiye da 50 yayin wasu jerin hare-hare da mayaƙan Boko Haram suka ƙaddamar kusan lokaci guda a kan garuruwan daban daban a jihohin Borno da Yobe.
Shirin ya waiwayi wasu daga cikin lamurran da suka wakana a Kamaru inda ake cigaba da dakoon Kotun Fasalta Kundin tsarin mulki ta tabbatar da sakamakon zaɓen shugabancin ƙasar.
A yankin gabas ta tsakiya, Amurka ta hau kujerar naki kan yunƙurin wasu na ganin Isra’ila ta kwace iko ya yankin Falasɗinu na Gaɓar yamma da kogin Jordan.