
27 December 2025
Najeriya ta tabbatar da harin da Amurka ta kai a wasu yankuna na jihar Sokoto
Mu Zagaya Duniya
About
A cikin daren ranar Alhamis da ta gabata Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da harin da Amurka ta kai a wasu yankuna biyu na jihar Sokoto wato Tangaza inda nan ne ‘yan Lakurawa ke da maɓoya da kuma Jabo da ke yankin ƙaramar hukumar Tambuwal.
Sai dai mazauna yankin Jabo sun bayyana fargabar zama a ƙauyukansu saboda fargabar yin kuskuren kai musu farmaki a yayin wasu hare-haren da watakila Amurkar ka iya kai wa a nan gaba.