29 August 2026
Adadin mutanen da suka mutu a ambaliyar ruwan Nepal na ci gaba da ƙaruwa
Mu Zagaya Duniya
About
Shirin ''Mu Zagaya Duniya" tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako, ya taɓo muhimman batutuwan da suka faru a makon da muke bankwana da shi, inda ya taɓo yadda ƴanbindiga suka yi awun gaba da mutum sama da 600 a wani kauye da ke kan iyakar Najeriya da Benin a can jihar Neja. Adadin mutanen da mumunar ambaliyar ruwa ta kashe a Nepal ya haura zuwa 470.
A ɓangaren wasanni kuwa, shirin ya yi waiwaye kan rahoto murabus ɗin shugabancin hukumar kwallon kafa ta Najeriya da kuma yadda aka gudanar da bikin ranar Hausa.
Ku latsa lamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna..........