
Zubar hazo a lokacin zafi ya haddasawa mutane da dama rashin lafiya a Kamaru
Lafiya Jari ce
A wannan makon shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan sauyawar yanayin da wani yanki na arewacin ƙasar Kamaru ya gamu da shi a watan Fabarairun da ya gabata wanda ba safai aka saba ganin faruwarsa ba, ta yadda ake ganin zubar hazo a wani yanayi da kuma ake fama da tsananin zafi, wanda ya haddasa cutuka, lamarin da ya sanya gamayyar masana lafiya dana yanayi jan hankali jama’a don su ɗauki matakan baiwa lafiyarsu kariya.
Tsawon kwanaki aka ɗauka hazo na sauka wanda ya mamaye yankuna da dama na arewacin Kamaru dai dai lokaci da zafi ke kaiwa maki 40 zuwa 45 a ma’aunin celsius wanda ya sanya fargabar famtsamuwar cutuka a yanki, lamarin da tuni ya sanya ƙaruwar masu fama da lalure-lalure na lafiya kama daga mura da kuma zazzaɓi har da tashin tsaffin cutukan da ƙura kan tunzura su.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.