
01 December 2025
Kamaru ta yi nasarar rage mutuwar mata yayin haihuwa a cikin shekaru 4
Lafiya Jari ce
About
A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan wasu alƙaluma da ke nuna cewa cikin shekaru 4 da suka gabata Kamaru ta yi nasarar rage yawan matan da ke mutuwa a lokacin haihuwa ko kuma goyon ciki.
Alƙaluman hukumar kula da lafiyar yara da na DHS mai tattara alƙaluman jama’a sun nuna da cewa da kusan rabi ne aka samu raguwar mace-macen matan, inda daga mace-macen mata dubu 2 cikin dubu 100 a 2018 adadin a yanzu ya dawo mace-macen mata 406 cikin dubu 100 duk shekara wanda ke nufin gagarumar nasara, kodayake ministan lafiya na ƙasar Manaouda Malachie ya ce sun yi amfani da wasu tsare-tsare gabanin samun wannan nasara.