Skip to content
Opens in a new window
Jamhuriyar Nijar ta shirya rigakafin cutar farar masassara a sassan ƙasar
26 October 2026

Jamhuriyar Nijar ta shirya rigakafin cutar farar masassara a sassan ƙasar

Lafiya Jari ce

About

Shirin na lafiya jari ce a wannan mako, zai yi duba ne kan babbar gayyar allurar rigakafin cutar farar masassara ko kuma Yellow fever da kasar Niger ta shirya a wasu jahohi da nufin daƙile yaɗuwar cutar tsakanin jama'arta.

Cutar farar masassara ko Yellow fever na cikin jerin cutuka masu haɗari da kan yaɗu cikin gaggawa tare da kisa ba ƙaƙƙautawa wannan ya sa da zarar aka ga ɓullarta, kai tsaye akan ayyanata a matsayin annoba, inda alƙaluma ke nuni da cewa a duk shekara mutum dubu 200 kan kamu da ita yayinda ta ke kashe dubu 30 zuwa 82 galibi a nahiyar Afrika.