
About
Shirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir a wannan mako ya mayar da hankali kan wasu alƙaluman mujallar Lancet da ke nuna cewa nan da shekarar 2050 fiye da kashi 50 na yawan al’ummar Afrika musamman Afrika za su zama masu ƙibar da ta wuce ƙima ko kuma Obesity a turance.
Alƙaluman na Lancet wanda aka tattara bayan gwaji a ƙasashe fiye da 50 ya nuna cewa matsloli masu alaƙa da cimaka da kuma rashin motsa jiki su ke matsayin kan gaba da za su haddasa wannan matsala ta Obesity ko kuma ƙibar da ta wuce ƙima.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.