Opens in a new window
Illar cushen kusan naira tiriliyan 1 a kasafin kuɗin Najeriya ga tattalin arziƙi
29 July 2026

Illar cushen kusan naira tiriliyan 1 a kasafin kuɗin Najeriya ga tattalin arziƙi

Kasuwanci

About

Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako, ya mayar da hankali ne kan yadda aka gano cushen kusan Naira triliyan ɗaya cikin kasafin kuɗin Najeriya na wannan shekarar ta 2026, domin sayen motocin alfarma da kuma ayyukan tallafa wa jama'a.

Wannan na ƙunshe ne cikin wani rahoton da wata  cibiyar da ke sa’ido kan yadda gwamnati ke kashe kuɗaɗen kasafi a Najeriya wato Tracka.

Cibiyar ta ce adaɗin ya zarce jimillar kuɗin da aka ware wa manyan ma'aikatun gwamnatin tarayya guda bakwai. Batu da ya janyo ce-ce-ku-ce.

A cikin rahotonta, Cibiyar ta nuna cewa gwamnatin ta ware kusan Naira biliyan 960 ga ma'aikatun Sufurin Jiragen Sama, Gidaje, Harkokin Mata, Ciniki da Masana'antu, Shari'a, Kiwon Dabbobi da Albarkatun Man Fetur, amma kuma ta ware kusan Naira biliyan 963 domin sayen motoci da kuma ayyukan tallafa wa jama'a.

Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.