Yadda satar jarabawa da cin hanci da rashawa ke kassara ɓangaren Ilimi a Kamaru
27 January 2026

Yadda satar jarabawa da cin hanci da rashawa ke kassara ɓangaren Ilimi a Kamaru

Ilimi Hasken Rayuwa

About

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda wani bincike can a Jamhuriyyar Kamaru ya gano yadda satar Jarabawa da cin hanci da rashawa ke mummunan tasiri a ɓangare ilimin ƙasar.

Matsalar ta cin hanci da rashawa kai tsaye ta yi mummunar illa ga yanayin ɗaukar malamai aiki da gina makarantu ko kuma samar da ci gaba a ɓangaren na Ilimi, yayinda a gefe guda satar jarabawar da ɗalibai ke yi ke zagon ƙasa ga makomar ilimi a ƙasar.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.