Makomar karatu a yankin arewacin Najeriya cike da barazanar ƴanbindiga
20 January 2026

Makomar karatu a yankin arewacin Najeriya cike da barazanar ƴanbindiga

Ilimi Hasken Rayuwa

About

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali kan makomar karatun ɗalibai a makarantun Najeriya musamman yankin arewaci mai fama da matsalolin tsaro, dai dai lokacin da aka koma sabon zangon karatu Iyaye na cike da fargaba kan tsaro a makarantu.

Makwanni gabanin tafiya hutun zangon da ya gabata cikin watan Nuwamban bara ne, hare-haren ƴan bindiga suka tilasta kulle makarantu a sassan arewacin Najeriyar ciki har da makarantun Unity da ke ƙarƙashin kulawar gwamnatin Tarayya.

Wasu na da ra'ayin cewa sai an haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin dukkanin ɓangarori ne, ɗalibai za su samu cikakken tsaro a makarantu tare da samun ɗorewar Ilimi a yankin.

Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.