
An yafe wa ɗaliban da ke son shiga kwalejin ilimi rubuta JAMB a Najeriya
Ilimi Hasken Rayuwa
A yau muna ɗauke da wani labari mai daɗi ga ɗaliban da ke sha’awar zama malamai da kuma masu son shiga Kwalejin Ilimi a faɗin Najeriya.
Gwamnatin ta fitar da wasu sabbin tsare-tsare da nufin sauƙaƙa wa ɗalibai hanyar neman ilimi da kuma ƙarfafa musu gwiwa ta fuskar kuɗi.
Ministan Ilimi Tunji Alausa, ya sanar da cewa ɗaliban da ke son shiga Kwalejin Ilimi yanzu ba sai sun rubuta jarrabawar UTME ba.
Amma dole ne ɗalibi ya kasance yana da aƙalla darussa biyar a sakamakonsa na sakandare. Duk da cewa ɗalibi ba zai rubuta jarrabawa ba, dole ne ya yi rajista da hukumar JAMB don tantance takardunsa domin samun gurbin karatu ta tsarin CAPS.
Bayan rage wa ɗalibai wahalar jarrabawa, gwamnatin ta kuma samar da tallafin karatu domin jawo hankalin kwararru zuwa fannin koyarwa. inda ta amince da biyan ɗaliban da ke karatu a kwalejojin ilimi na gwamnati alawus din naira naira 50,000 a kowane zango, waɗanda ke karatun digiri a fannin ilimi a jami’o’in gwamnati za su samu naira naira 75,000
Masana a fannin ilimi dai na ganin cewa, wannan wata babbar dama ce ga iyaye da ɗalibai da ya kamata su yi amfani da ita don sauƙaƙa wa kansu nauyin kuɗi da kuma samun gurbin karatu cikin sauƙi.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shrin