
About
A Najeriya, jam’iyyun siyasa sun kammala zaɓen fidda ƴantakarar da za su tsaya musu a matakai daban-daban na zaɓukan da za a yi cikin shekara mai zuwa. To sai dai a ɓangaren adawa, mafi yawan jam’iyyun sun gudanar da zaɓukan ne a cikin yanayi na rabuwar kawuna sakamakon rikicin shugabanci.
To akwai yiyuwar wannan rikici na cikin gida ya iya shafar ƙima da kwarjinin adawa a zaɓukan na baɗi?
Shiga alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya yi wa Farfesa Usman Mohammed, masani siyasa a Najeriya.