Tattaunawa kan shirin Najeriya na maido da tsoffin sojoji don tabbatar da tsaro
30 January 2026

Tattaunawa kan shirin Najeriya na maido da tsoffin sojoji don tabbatar da tsaro

Bakonmu a Yau

About

A farkon makon nan, gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin maido da tsaffin sojoji bakin aiki, domin taimaka wa wajen samar da tsaro a yankunan da ke fuskantar barazanar ƴan ta’adda a sassan ƙasar.

Sanar da matakin na zuwa ne bayan kafa wani kwamiti mai mambobi 18 da ministan tsaron na Najeriya Janar Chrisroper Musa mai ritaya ya jagoranci samarwa, wanda ya ce aikinsa shi ne tabbatar da ƙwato dukkanin yankunan da ke ƙarƙashin ikon ƴan ta’adda.

Dangane da wannan Nura Ado Suleima ya tattauna da Dakta Auwal Aliyu Abdullahi, mai magana da yawun Kwamitin musamman da ke kula da walwalar tsaffin sojoji a Najeriya.