21 October 2026
Tattaunawa da Pharmacist Ayuba Tanko kan hukunta masu samar da magungunan jabu
Bakonmu a Yau
About
Ƙungiyar Jami'an kula da magunguna da PSN a Najeriya ta buƙaci gwamnatin ƙasar da ta tsaurara dokar hukunta kamfanoni da ɗaiɗaikun mutanen da ke sarrafa magunguna na bogi waɗanda ke sanadiyyar salwantar rayukan jama'a
Shugaban ƙungiyar na ƙasa Pharmacist Ayuba Tanko Ibrahim ya ce suna buƙatar sanya tarar miliyan 5 tare da ɗaurin rsakanin shekaru 5 zuwa 20 a kan duk wanda aka samu samu da aikata irin waɗannan laifuka, saɓanin tarar naira dubu biyar zuwa goma da ake karɓa a hannun masu laifin yanzu bisa tanadin dokokin Najeriya.
Kan hakan ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban ƙungiyar na ƙasa Pharmacist Ayuba Tanko Ibrahim.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar zantawarsu.