
21 January 2026
Tattaunawa da Injiniya Datti Yusuf Yahya kan kafa matatun zinare a Najeriya
Bakonmu a Yau
About
Makomar ayyuka da tsarin haƙar ma’adanai na cikin batutuwan da a ‘yan kwanakin nan ya ɗauki hankali a Najeriya, inda a gwamnatin ƙasar ta musanta zargin cewa tana shirin kafa matatar zinare mallakinta a jihar Legas da ke kudancin ƙasar.
Tun da fari, ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya ce ta yi wannan ƙorafi cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa, inda ta bayyana matakin a matsayin rashin adalci, la’akari da cewar yankunan arewa maso yammaci da tsakiyar Najeriya ne ke da arzikin na Zinare.
Kan wannan da wasu batutuwan masu nasaba, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Injiniya Datti Yusuf Yahya ƙwararre kuma tsarawa da bayar da shawara kan ayyukan haƙar ma’adanai a Najeriya.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawar.