Tattaunawa da Fatima Dangote kan shirin faɗaɗa aikin matatar Ɗangote
27 October 2025

Tattaunawa da Fatima Dangote kan shirin faɗaɗa aikin matatar Ɗangote

Bakonmu a Yau

About

Katafaren kamfanin Dangote, ya sanar da shirin faɗaɗa matatar sa mai samar da tacaccen gangar mai 650,000 zuwa miliyan guda da 400,000 a kowacce rana. 

Shugaban rukunin kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya ce za'a kwashe shekaru uku ana aikin faɗaɗa matatar wadda ya ce za ta zama mafi girma a duniya. 

Dangane da wannan ci gaba ne kuma Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da babbar manajar rukunonin kamfanin, Fatima Aliko Dangote.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.....