
About
Ga dukkanin alamu akwai yiwuwar yaƙi tsakanin Iran da kuma haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila ya ɗauki tsawon lokaci saɓanin zaton da ake yi na ya kasance gajere, wannan kuwa ya biyo bayan jawabin shugaban Amurka Donald Trump a daren jiya da ke cewa mai yiwuwa a shafe makwanni 4 zuwa 5 suna kai hare-hare kan Iran.
Wannan na zuwa ne a yayin da yaƙin da ya rincaɓe, ke ci gaba da shafar ƙasashe da dama a Yankin Gabas ta Tsakiya.
Domin jin yadda masana siyasar ƙasa da ƙasa ke kallon lamarin, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Farfesa Tukur AbdulƘadir na Jami’ar Jihar Kaduna a Najeriya.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar..