Tattaunawa da  Farfesa Tijjani Naniya kan matsayar taron AU game cinikin bayi
17 February 2026

Tattaunawa da Farfesa Tijjani Naniya kan matsayar taron AU game cinikin bayi

Bakonmu a Yau

About

Masana Tarihi gami da Siyasar Duniya sun fara yin tsokaci kan matsayar da ƙungiyar ƙasashen Afrika AU ta tsaida na amincewa da ƙudurin bayyana cinikin bayi da kuma bautar da su gami da Mulkin Mallakar da Turawan yamma  suka yi wa Nahiyar a matsayini kisan ƙare dangi da kuma laifukan take hakkin ɗan Adam.

Shugabannin ƙasashen nahiyar ta Afrika sun cimma matsayar ce a Lahadin da ta gabata, yayin ƙarƙare taronsu na shekara karo na 39 a birnin Addis Ababa.

Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Farfesa Tijjani Muhd Naniya, masanin tarihi da ke jami’ar Bayero a Kano, Najeriya.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.