Skip to content
Opens in a new window
Tattaunawa da Datective Auwal Bala kan baiwa MOPOL damar yaƙi da ta'addanci
08 September 2026

Tattaunawa da Datective Auwal Bala kan baiwa MOPOL damar yaƙi da ta'addanci

Bakonmu a Yau

About

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta sanar da tsaurara matakan yaƙi da ta’addanci da ya addabi ƙasar ta hanyar shigar da ƴan sandan kwantar da tarzoma cikin aikin fatattakar ƴan ta’adda.

Da yake jawabi yayin wani rangadi da ya kai barikokin ƴan sanda a jihar Lagos, babban sufeton ƴan sandan ƙasar Tunji Disu ya ce, daga yanzu za’a sanya jami’an cikin aikin gadan-gadan.

Game da wannan batu Rukayya Abba Kabara ta tattauna Datective Auwal Bala masanin tsaro a Najeriya.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.