
About
A Najeriya, gobe Alhamis 1 ga watan Janairu ne, za a fara aiwatar da sabuwar dokar haraji ta ƙasa, a cikin yanayi da dokar ke shan suka saboda dalilai da dama.
Yayin da jama’a ke cewa sabon tsarin karɓar haraji na matsayin ƙarin nauyi ne ga al’umma, hakazalika wasu ƴan majalisa sun yi zargin cewa abin da suka amince da shi ya sha bambam da abin da gwamnati ke shirin aiwatarwa.
A game da shirin aiwatar da dokar ne Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Dakta Mahdi Shehu da ke fafutuka a Najeriya, ga kuma zantawarsu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.