
About
Amurka ta kawo ƙarshen tallafin da ta ke bayar wa a hukumar Lafiya ta Duniya WHO daga wannan Alhamis, 22 ga watan Janairun 2026, duk kuwa da kasancewarta jigo wajen samar da kuɗaɗen tafiyar da hukumar wadda ke samar da tallafin magunguna da sauran ɓangarorin lafiya ga ƙasashe da dama musamman masu tasowa.
Donald Trump ya sanar da aniyar janyewar ƙasar daga hukumar koda yake tun a wancan lokaci ya ƙulla yarjejeniyar cewa sai bayan shekara guda ne ficewar za ta fara aiki a hukumance.
Kan haka ne Faruk Muhammad Yabo ya tattauna da Dr Adam Mustapha na sashen nazarin ƙananan halittu a jami’ar Maiduguri ya yi mana tsokaci kan illar da matakin na Amurka ka iya haifarwa.