Skip to content
Opens in a new window
Tattaunawa da Barr Abdullahi Jalo kan gano musabbabin mutuwar masu haƙar ma'adinai a Neja
28 October 2026

Tattaunawa da Barr Abdullahi Jalo kan gano musabbabin mutuwar masu haƙar ma'adinai a Neja

Bakonmu a Yau

About

Kwamitin binciken da gwamnatin Najeriya ta kafa domin gano dalilan da suka yi sanadiyyar mutuwar mahaƙan zinare 33 a komar hukumar tsaron Civil defence a birnin Minna na jihar Neja ya bayyana cewa rashin iska ne ya sanya matasan sumar da ya kai ga rasa rayukansu yayinda wasu 44 kuma galabaita kodayake an yi nasarar ceto rayuwarsu.

Kwamitin ya buƙaci biyan diyya kan dukkanin mamatan 33 baya ga 44 da suka tsira da rayukansu yayinda kuma ya bayar da shawarar gaggauta korar kwamandan rundunar ta Civil Defence a jihar Neja dama ialhirin jami'an da suka kai ga wannan sakaci.

Barr Abdullahi Jalo na ɗaya daga cikin dattawan da suka buƙaci gudanar da binciken gaggawa lokacin afkuwar lamarin kuma Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shi bayan fitar wannan sakamakon bincike.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawarsu....