Opens in a new window
Tattaunawa da Barista Umar Ɗanbaito kan ƙaruwar ƙasashen da ke ficewa daga ICC
29 July 2026

Tattaunawa da Barista Umar Ɗanbaito kan ƙaruwar ƙasashen da ke ficewa daga ICC

Bakonmu a Yau

About

Chadi ta zama ƙasa ta biyar da ta bi sahun ƙasashen da suka bayyana aniyar ficewa daga ƙarƙashin kotun hukunci kan manyan laifuka ta Duniya ICC.

A jiya Litinin ne dai gwamnatin Chad ta sanar da fara shirin, saboda abinda ta kira gazawar kotun Duniyar wajen sauke nauyin da ke wuyanta, inda ta fi karkata hukunce-hukuncenta kan ƙasashen Afrika.

Don jin yadda masana dokoki ke kallon wannan lamari, da kuma makomar Kotun Duniyar, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Barista Umar Usman Ɗanbaito da ke Najeriya.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawar.