
About
Daukacin kasashe 55 dake cikin hukumar kwallon kafar Turai sun kaɗa kuri'ar kin amincewa da shirin sayar da hannayen jarin FIFA, tare da barazanar kauracewa wasannin cin kofin duniyar da za'a gudanar nan gaba.
Kasashen sun yi fatali da shirin shugaban FIFA Gianni Infantino na sayar da kashi 20 na hannun jarin kamfanin. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Tsohon Sakatare Janar na hukumar kwallon kafar Najeriya, Hon Sani Ahmed Toro.
Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...