Prof Tukur Abdulƙadir kan cika shekaru 4 da faro yaƙin Rasha da Ukraine
25 February 2026

Prof Tukur Abdulƙadir kan cika shekaru 4 da faro yaƙin Rasha da Ukraine

Bakonmu a Yau

About

Shugabannin ƙasashen ƙungiyar Tarayyar Turai EU, sun sha alwashin babu gudu babu ja da baya, kan ci gaba da taimaka wa Ukraine a yaƙin da take yi da Rasha. A yayin da ita kuma Rashar ta lashi takobin ci gaba da yaƙi har ta cimma nasarar da take nema, bayan da ta amince cewar zuwa yanzu ta gaza cimma muradunta a maƙwafciyar tata. 

Waɗannan ɓangarori sun bayyana matsayarsu ce bayan cika shekaru huɗu cif da ɓarkewar yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine, a rana mai kamar ta jiya Talata, 24 ga watan Fabarairun shekarar 2022.

Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Farfesa Tukur Abdulƙadir na Jami’ar Jihar Kaduna da ke Najeriya, wanda ya yi tsokaci kan yadda lamura ke warwara.

Ku latsa alamar sauti don jin yadda tattaunawarsu ta gudana...............