Majalisa ta ƙara yawan kuɗaɗen da 'yan takara zasu iya kashewa a yaƙin neman zaɓe
19 December 2025

Majalisa ta ƙara yawan kuɗaɗen da 'yan takara zasu iya kashewa a yaƙin neman zaɓe

Bakonmu a Yau

About

Majalisar wakilan Najeriya ta gudanar da wasu sauye-sauye ga dokar zaɓen ƙasar yayin zaman da ta yi a jiya Alhamis. Kuma daga cikin batutuwan da suka fi ɗaukar hankali akwai ƙara yawan kuɗaɗen da doka ta ƙayyade ɗan takara zai iya kashewa a yaƙin neman zaɓe, da kuma tilasta amfani da na’urorin tantance masu kaɗa ƙuri’a, gami da watsa sakamakon zaɓe kai tsaye.

Sauyin dai na nufin daga yanzu masu neman shugabancin ƙasa na iya kashe Naira biliyan 10, saɓanin Naira biliyan 5, yayin da aka ƙara kasafin ‘yan takarar gwamna daga Naira Biliyan 1 zuwa biliyan 3.

Domin jin yadda masana doka ke kallon wannan mataki, Nura Ado Suleiman ya tuntuɓi Barista Al-Zubair Abubakar da ke Najeriya.

Latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana...