Skip to content
Opens in a new window
Kamilu Sani Fagge kan tsanantar rikici a Gabas ta tsakiya
10 September 2026

Kamilu Sani Fagge kan tsanantar rikici a Gabas ta tsakiya

Bakonmu a Yau

About

Rikicin Gabas ta Tsakiya da ya tsananta tsakanin Amurka da Iran na cigaba da faɗaɗa, inda a ‘yan kwanakin nan ya kai ga sake tayar da rikicin Yemen tsakanin gwamnatin ƙasar da Saudiya ke marawa baya, da kuma ‘Yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran, ɓangarorin da zuwa yanzu suka rasa mayaƙa fiye da 500.

Baya ga datse mashigin ruwan Hormuz, a halin yanzu rikicin na Gabas ta Tsakiya ya shafi mashigin ruwan Bab al-Mandeb da ke tekun Maliya, inda mayaƙan Houthi ke kai wa manyan jiragen ruwa farmaki don goyon bayan Iran.

Don jin yadda masana ke kallon lamarin da kuma haɗarin da ke tattare da shi, Nura Ado Suleima ya tattauna da Farfesa Kamliu Sani Fagge na jami’ar Bayero da ke Kano.