Skip to content
Opens in a new window
Kaftin Bakoji kan banbancin kudanci da arewacin Najeriya wajen tunkarar matsalar tsaro
05 October 2026

Kaftin Bakoji kan banbancin kudanci da arewacin Najeriya wajen tunkarar matsalar tsaro

Bakonmu a Yau

About

Wata matsala da masana tsaro ke tsokaci a kai a Najeriya, shi ne yadda ake samun banbanci tsakanin jihohin Arewacin ƙasar da na kudanci wurin tunkarar ƙalubalen tsaro a yayin da aka samu ibtila’i na garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa ko kuma hare-haren yan ta’adda.

Galibi dai jihohin kudancin Najeriya na matsawa gwamnatin tarayya a duk sanda irin wannan lamari ya faru ta yadda take aikewa da manyan jami’an tsaro cikin gagagwa domin tabbatar da ganin an daƙile matsalar idan ta faru a yankin kudanci, amma  a Arewacin kasar har kawo yanzu akwai daruruwan mutane da aka gaza ceto su daga hannun yan bindiga.

Kan haka wakilinmu Ƙaribullah Abdulhamid Namadobi ya tattauna da Kyaftin Abdullahi Bakoji Mai-Ritaya kan ko me ya kawo wannan banbanci?

Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...