Skip to content
Opens in a new window
Ibrahim Salissou kan tura sojojin Aljeriya zuwa Nijar da za a yi
26 October 2026

Ibrahim Salissou kan tura sojojin Aljeriya zuwa Nijar da za a yi

Bakonmu a Yau

About

Majalisun dokokin Aljeriya, sun bai wa gwamnati damar tura sojojin ƙasar zuwa  Jamhuriyar Nijar, kwanaki uku bayan da ministocin ƙasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro a tsakaninsu. Aljeriya da Nijar ƙasashe ne da suka raba iyakar mai tsawon sama da kilomita 900, yayin da ake kallon yankin iyakar a matsayin wanda fatake ke amfani da shi domin gudanar da safara iri-iri.

Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da mai magana da yawun ƙawancen wasu ƙungiyoyin da ke fafutukar ƴantar da nahiyar Afirka FRSA, Ibrahim Salissou, domin jin yadda suke kallon wannan batu na bai wa Aljeriya damar jibge sojoji a Nijar.

Ku latsa alamar sauto domin jin yadda tattaunawarsu ta kasance...........