About
A ranar Litinin da ta gabata, matatar man fetur ta Ɗangote ta dasa ɗambar shirinta na shiga kasuwar hada-hadar hannayen jari, waɗanda shugaban rukunin kamfanonin na Ɗangote, Alhaji Aliko, ya ce ana iya mallakar aƙalla guda 10 da ƙasa da Naira dubu 6.
Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Honorable Sama’ila Mohammed, masanin tattalin arziƙi a Najeriya, wanda ya yi tsokaci kan tasiri da kuma yadda ‘yan Najeriya musamman masu ƙaramin ƙarfi za su amfana sayen hannayen jarin matatar man ta Ɗangote.
Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu..............