Hira da Kailani Muhammad kan baiwa China ragamar farfaɗo da matatun man Najeriya
06 May 2026

Hira da Kailani Muhammad kan baiwa China ragamar farfaɗo da matatun man Najeriya

Bakonmu a Yau

About

Kamfanin mai na NNPC ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da wasu kamfanonin ƙasar China guda biyu, Sanjiang Chemical Company Limited da kuma Fuzhou Industrial Park, domin farfaɗo da matatun mai na Warri da Port Harcourt.

Wannan mataki ya zo ne bayan matatun man sun laƙume kimanin biliyan 3.2 na dala ba tare da an samu biyan buƙata ba.

Injiniya Kailani Muhammad, tsohon babban jami’in kamfanin na NNPC ne, a tattaunawarsa da Shamsiyya Haruna, ya bayyana gamsuwa da wannan yarjejeniya da kasar China bisa wasu dalilai.

Ku latsa alamaru sauti don sauraren cikakkiyar hirar.