Halin da ƙasashen AES ke ciki, shekaru biyu bayan ficewa daga cikin ECOWAS
29 January 2026

Halin da ƙasashen AES ke ciki, shekaru biyu bayan ficewa daga cikin ECOWAS

Bakonmu a Yau

About

Yau ake cika shekaru biyu da ficewar ƙasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso daga cikin ECOWAS, KO CEDAEO, biyo bayan matsin lambar ƙungiyar ta yi musu saboda juyin mulkin da sojojinsu suka yi, da kawar da matsalolin da suka zargi gwamnatociin da suka hamɓarar da gaza magancewa.

Domin tsokaci kan halin da ƙasashen na AES ke ciki, shekaru biyu bayan matakan da mahukuntansu suka ɗauka, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Abdel Nasser Saidu ɗaya daga cikin wakilan kungiyoyin farraren fula a Nijar..