Skip to content
Opens in a new window
Farfesa Muhammad Dukku kan gazawar jihohi wajen karɓar tallafin inganta Makarantu
13 August 2026

Farfesa Muhammad Dukku kan gazawar jihohi wajen karɓar tallafin inganta Makarantu

Bakonmu a Yau

About

Hukumar kula da ilimin Firamare a Najeriya ta roƙi gwamnonin ƙasar da su yiwa Alla su je su karɓi naira biliyan 332 waɗanda yanzu haka ke ajje a Banki, domin inganta ilimi a jihohinsu.

Shugabar hukumar Aisha Garba ta ce baya ga naira biliyan 65 da aka ware domin kai ɗaukin gaggawa, akwai kuma naira biliyan 267 da ke ajje domin amfanin jihohin.

Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Muhammad Dukku, tsohon shugaban hukumar kula da ilimin Firamare a jihar Gombe ga kuma tattaunawarsu.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.......