Farfesa Mansur Idris kan raguwar bashin da China ke baiwa ƙasashen Afrika
28 January 2026

Farfesa Mansur Idris kan raguwar bashin da China ke baiwa ƙasashen Afrika

Bakonmu a Yau

About

Wani sabon rahoton masana, ya nuna cewar yawan tallafin bashi da China ke bai wa ƙasashe marasa ƙarfi musamman na Afrika ya ragu matuƙa daga kashi 124 cikin shekaru 10 da suka gabata zuwa kashi 56.

A cewar rahoton, wannan na zuwa ne , a yayin bashin da ƙasashen na Afrika suke biyan ƙasar ta Sin ke ci gaba da ƙaruwa, fiye da tallafin da suke samu daga gareta ba. Ga misali a tsakanin 2000 zuwa 2023 China ta tallafa wa ƙasashen Afrika 49 da bashin Dala biliyan 182, to amma a shekarar 2024, tallafin Dala Biliyan 2.1 kawai ta samar.

Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna na Farfesa Mansur Idris na Jami’ar Bayero da ke Kano.

Shiga alamar sauti domin sautraron cikakkiyar tattaunawar.