Dr Yahuza Getso kan harin da Amurka ta kai jihar Sokoto ta arewacin Najeriya
26 December 2025

Dr Yahuza Getso kan harin da Amurka ta kai jihar Sokoto ta arewacin Najeriya

Bakonmu a Yau

About

Da sanyin safiyar yau Juma’a aka wayi gari da sanarwar gwamnatin Najeriya da ke tabbatar da harin da Amurka ta kai a wasu yankunan ƙananan hukumomin Tambuwal da Tangaza, da ke jihar Sokoto a yankin arewa maso yammacin ƙasar.

Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar, ya ce Amurka ta kai hare-haren ne tare da haɗin gwiwar dakarun ƙasar, a wani ɓangare na ƙawancen da suka ƙulla da zummar murƙushe ta’addanci.

Dangane da wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Yahuza Gesto masanin tsaro da ke tarayyar Najeriya.

Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawar...