
About
Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa za ta fara kwashe ƴan ƙasarta da ke son komawa gida daga Afirka ta Kudu, matakin da ta ce ya zama dole saboda tsananin kyamar baƙi da kuma rahoton mutuwar wasu ƴan Najeriya biyu sakamakon hare-haren da ake kai wa ƴan cirani.
Akalla 'yan Najeriya 130 ne suka riga suka yi rajista don neman a kwashe su zuwa gida, sakamakon fargabar makomarsu na rashin tabbas.
Dakta Rakiya Sa’idu daga jami’ar Capetown, ta bayyana mana yadda ƴan siyasa ke amfani da lokacin zaɓe wajen rura wutar wannan matsala.
Ku latsa alamar sauti don jin tattaunawar da Shamsiyya Haruna ta yi da ita............