
20 January 2026
Dr AbdulHakim Funtua kan cika shekara guda da Trump ya yi kan karagar mulki
Bakonmu a Yau
About
Yau Donald Trump ke cika shekara guda da komawa shugabancin Amurka, wa’adin da wasu ke ganin tamkar shugaban ya shafe shekara da shekaru bisa mulkin, la’akari da jerin matakan da ya riƙa aiwatarwa a matakin ƙasa da ƙasa da kuma cikin gida, ba tare da la’akari da caccakar da ake yi masa ba a gida da waje.
Domin jin hasashen masana kan abinda ke tafe a ragowar shekaru uku da suka rage wa shugaban na Amurka Donald Trump, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta AbdulHakim Garba Funtua masanin siyasar ƙasa da ƙasa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron zantawarsu...........