About
Ƙungiyar Amnesty International ta bayyana damuwa game da yadda ake kama ƴan adawa ana tsarewa a jihar Borno dake Najeriya ba tare da aikata laifuffuka ba.
Ƙungiyar ta bayyana matakin a matsayin wani yunkuri na tirsasawa jama’a bayyana ra’ayoyin su da suka saɓa da na hukuma, musamman ganin yadda aka kama wasu matasa 11 aka tsare a gidan yarin Maiduguri, cikin su harda biyar da suka sanya rigar dake buƙatar shugaban ƙasa Bola Tinubu ya tafi wato ƴan 'Tinubu Must Go' a turance.
Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Isa Sanusi, Daraktan Ƙungiyar a Najeriya.
Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawar...