
24 February 2026
Dakta Kabiru Adamu kan fatan samar da cibiyar sauya tunanin tubabbun ƴan bindiga
Bakonmu a Yau
About
Gwamnatin Jihar Benue a Najeriya, na neman amincewar gwamnatin tarayyar ƙasar wajen gina cibiyar sauya tunanin ‘yan bindigar da suka tuba, da ma sauran mutanen da wani yanayi ya sanya su taimaka wa ayyukan ta’addanci, ciki kuwa har da mata waɗanda ke yi wa ‘yan ta’addan aiki a bisa tilas bayan garkuwar da aka yi da su.
Wannan na zuwa ne a yayin ake ci gaba da samun banbancin ra’ayi tsakanin ‘yan Najeriya a kan irin wannan yunƙuri.
Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Consulting da ke bincike kan tsaro a nahiyar Afrika.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar..